Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha-Syria

Kawancen 'yan tawaye ya kaddamar da farmaki kan mayakan IS

Sabon kawancen kungiyoyin ‘yan tawayen Syria da Amurka ke marawa baya, ya kaddamar da hare-hare akan mayakan kungiyar da ke ikirarin jihadi a lardin Hasaka da ke Syria, kwana daya bayan da Amurka ta sanar da aikewa da sojojinta na kasa 50 zuwa kasar.

'Yan tawaye a kusa da barikin sojan sama na Nairab a garin Aleppo na Syria
'Yan tawaye a kusa da barikin sojan sama na Nairab a garin Aleppo na Syria Reuters/Hosam Katan
Talla

Wannan sabon kawance mai suna Democratic Forces of Syria wanda ya kunshi Kurdawa da wasu Larabawan Syria, wadanda ke samun horo da kuma shawarwari daga Amurka.

A ranar juma'a da ta gabata Amurka ta sanar da tura sojointa sama da 50 zuwa arewacin kasar ta Syria domin taimaka wa wadanda take kira 'yan adawa masu sassaucin ra'ayi domin fada da mayakan ISIS da kuma dakarun Bashar Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.