Isa ga babban shafi
Myanmar

Jam'iyar Aung San Suu Kyi ta lashe mafi yawan kujeru a majalisar dokokin kasar

Hukumar  Zaben  kasar Myanmar ta bayyana kammalalen sakamakon zaben kasar wanda ya nuna cewar Jam’iyar Aung San Suu Kyi ta samu gagarumar nasara a tarihin siyasar kasar.

Madigar yan adawar kasar Myanmar  Aung San Suu Kyi ke gaida magoya bayanta a lokacin yakin neman zaben kasar
Madigar yan adawar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ke gaida magoya bayanta a lokacin yakin neman zaben kasar Reuters/路透社
Talla

Hukumar zaben kasar tace Jam’iyar NLD ta samu kujerun Majalisa 348 wanda zai bata jagorancin kasar ba tare da wata matsala ba.

Tuni shugabanin duniya suka fara aikewa da sakon taya murna ga shugabar jam’iyyar.

Wannan nasara dai, zata baiwa madigar yan adawar kasar ta Myamar, Aung San Suu Kyi damar kafa gwamnati a kasar, baya da a baya ta share tsawon lokaci tsare a kurku ga hannun mahukumtan mulkin sojan kasar ta Myamar, nada jan aiki a gabanta wajen yayyafa ruwa a wutar tashin hankalin kabilanci da addini dake faruwa yanzu haka tsakanin mabiya addinin Buda, da musulmin kasar, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, da suka hada da mata da yara, a yayinda wasu dubbai suka gujewa gidajensu
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.