Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin Taliban a Kandahar ya hallaka mutane 50

A kasar Afghanistan an tabbatar da mutuwar mutane 50 daga munmunar harin da mayakan Taliban suka kai a filin tashin jiragen sama dake Kandahar.‘Yan kunar bakin wake 11 ne suka yi nasarar kutsawa filin tashin jiragen saman inda suka yi ta tada bama baman da ke daure a jikin su a tsakiyar jama’ar da su kayi garkuwa da su.

Fillin tashin Jirgin  Kandahar dake Afghanistan
Fillin tashin Jirgin Kandahar dake Afghanistan AFP PHOTO/SHAH Marai
Talla

An kwashi tsawon awanni 27 mayakan Taliban na rike da ikon filin tashin jiragen kafin daga bisani jam’ian tsaro su iya kawo karshen hare haren da ya kasance mafi muni a tsawon shekaru 14 da kungiyar Taliban ta kaddamar da hare haren ta a kasar.

Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce cikin mutane 50 da suka rasa rayukansu akwai sojoji da ‘Yan sanda goma sauran kuma farraren hula ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.