Isa ga babban shafi
China

Mutane 91 sun bata a China sakamakon zabtarewar kasa

Kimanin mutane 91 suka bata sakamakon Zabtarewar kasar da aka samu a kasar China da ya yi sanadiyar birne gidaje sama da 30 tare da haifar da fashewar gas.

Zabtarewar kasa ta yi sanadin bacewar mutane da dama a China
Zabtarewar kasa ta yi sanadin bacewar mutane da dama a China REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Al’amarin ya shafi yankin Shenzhen, inda rahotanni suka ce zabtarewar ta janyo rusa gidaje da dama.

Masu aikin agaji sama da 1.500 aka tura domin ceto wadanda hadarin ya ritsa da su. Amma ruwan sama na kawo tsaiku ga aikin kamar yadda Kamfanin dillacin labaran China Xinhua ya ruwaito.

Ma’aikatar kula da filaye ta danganta matsalar da rashin ajiye kasar da ake gini ta hanyar da ya dace.

Masana kimiyar muhalli a China sun ce wannan ne karon farko da aka samu irin wannan zabtarewar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.