Taliban ta kashe Sojojin Amurka 6 a Afghanistan
Wani Dan kungiyar Taliban akan babur ya kashe sojojin Amurka guda shida a wani harin kunar bakin waken da ya kai musu a kusa da birnin Kabul da ke kasar Afghanistan.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce an kai harin ne lokacin da sojojin tare da wasu na Afghanistan ke sintirin hadin gwiwa, kuma tuni kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai harin.
Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da mayakan kungiyar ke kama garin Helmand inda gwamnan Yankin ya ce Taliban ta kama cibiyar ‘Yan Sandan garin da ofishin gwamna da kuma gine-ginen gwamnati.
Kame garin Helmand dai babban kalubale ne ga Sojojin Afghanistan wadanda ke jan ragamar tafiyar da tsaro a kasar bayan ficewa dakarun NATO.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu