Gobara ta hallaka mutane a asibitin Saudiya
Hukumomin Saudiya sun bayyana cewa wata gobara da ta tashi a wani babban asbiti da ke yankin kudancin kasar ta hallaka mutane 25 tare da jikkata 107.
Wallafawa ranar:
Tuni dai aka yi nasarar kashe gobarar wadda ta tashi a sahsen kula da mata masu juna biyu na asibitin Jazan kuma jami’an tsaro ne suka taimaka wajen kashe ta.
Al-ummar kasar na tofa albarkacin bakinsu dangane da tashin gobarar, inda wasu daga cikinsu suka caccaki hukumomin kasar a shafukan sada zumunta na internet sakamakon rashin kula da asibitin.
Wasu kuwa sun bukaci a sauke minitan lafiya na kasar Khalid al-Falih daga kujerarsa.
A watan Agustan da ta gabata mutane 10 sun rasa rayukansu yayinda sama da 200 suka jikkata sakamakon hatsarin gobara a wani babban gini da kamfanin man fetur na Aramco ke amfani da shi a yankin gabashin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu