Isa ga babban shafi
Saudiya-Iran

An yi zanga-zangar kin jinin Saudiya a Iran

An gudanar da zanga-zangar kin jinin Saduiya a Iran a jiya juma’a domin nuna adawa da kisan malamin shi’a da Saudiya ta yi da kuma zargin kasar da tarwatsa ofishin jekdancin Iran a Yemen.

Saudiya ta katse hulda da Iran
Saudiya ta katse hulda da Iran REUTERS
Talla

A Pakistan ma ‘Yan shi’a sun gudanar da zanga-zangar adawa da Saudiya a Islamabad.

Tuni dai Saudiya ta yanke hulda da Iran bayan an kona ofishin jekadancinta a Tehran kan kisan Malamin Shi’a Nimr al Nimr da aka zartarwa hukuncin kisa.

Ana ganin rikici dtsakanin Iran da Saudiya na iya haifar da rikicn banbancin akida tsakanin Sunni da Shi’a, matakin da kuma ke dada barazana ga kokarin kawo karshen rikicin Syria da Yemen da kasashen biyu ke jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.