Isa ga babban shafi
Taiwan

Girgizar kasa ta kashe mutane a Taiwan

Wata girgizar kasa mai karfin maki 6.4 ta auku a yankin kudancin Taiwan a cikin daren da ya gabata, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyar bayan ta rikito da wani gini mai hawa 16 yayin da ake fargabar cewa mutane fiye da talatin na makale karshin ginin da ya rubta.

Girgizar kasar ta rikito da gini mai hawa 16 a birnin Tainan na kasar Taiwan
Girgizar kasar ta rikito da gini mai hawa 16 a birnin Tainan na kasar Taiwan Foto: Reuters
Talla

Jami’an bayar da agajin gaggawa sun yi nasarar ceto mutane 200 daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su amma an kwantar da sama da 60 a asibiti.

Gairgizar kasar dai wadda ta ratsa karkshin kasa da kimanin kilomita 10 ta raunata mutane 316 a birnin Tainan kadai.

Hukumar gargadin aukuwar ambaliyar ruwan tsanami ta bayyana cewa babu alamar faruwar ambaliyar tsanami a kasar.

A watan satumban shekarar 1999 ne, girgizar kasa a Taiwan mai karfin maki 7.6 ta kashe kimanin mutane 2,400.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.