Isa ga babban shafi
SYRIA

Yau ake bude sabuwar tattaunawa kan rikicin Syria

Yau ake saran fara wata sabuwar tattauna tsakanin wakilan manyan kasahsen duniya da kuma bangarorin dake rikici a kasar Syria da zummar kawo karshen zub da jinin da aka kwashe shekaru biyar anayi.

Jakadan Majalisar dinkin duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura
Jakadan Majalisar dinkin duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Yanzu haka dai rikicin ya lakume rayukan mutane sama da 300,000 inji Majalisar Dinkin Duniya, yayin da sama da miliyan biyu suka zama 'Yan gudun hijira.

Ita dai wannan sabuwar tattaunar na zuwa ne a dai dai lokacin da ake yabawa bangarorin da ke rikici a Syria saboda yadda suka mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma baiwa jami’an aikin agaji kai kayan abinci Yankunan da rikicin ya ritsa da su.

Sai dai har yanzu ana tauna tsakuwa kan manufofin taron da kuma bukatun kowanne bangare.

Yayin da manyan kasahsen duniya da 'Yan adawar Syria ke bukatar ganin shugaba Bashar Al Assad ya sauka daga kujerar sa a yarjejeniyar da ake saran taron ya amince da shi nan da watanni 18 masu zuwa.

Ministan harkokin wajen Syria Walid al Muallem yace duk wani shiri na sauke shugaban zai zama wuce gona da iri.

Wadannan kamalai na shi ga alama sun yiwa Amurka da Faransa zafi, inda Sakataren harkokin wajen kasar John Kerry da takwaran sa Jean-Mark Ayrault suka bayyana shi a matsayin takala.

Kerry ya ce kasashen Russia da Iran sun amince da shirin gudanar da zabe a Syria da kuma mika mulki a tataunawar da za’ayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.