Isa ga babban shafi
India

Gada ta kashe mutane 25 a India

Rahotanni daga kasar India na cewa, kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 25 da suka rasa rayukansu sakamakon faduwar wata gada mai tsawon mita 100  a yankin gabashin kasar.  

Gadar ta fado ne a dai dai lokacin da jama'a ke hada-hada a birnin Kolkata na India
Gadar ta fado ne a dai dai lokacin da jama'a ke hada-hada a birnin Kolkata na India REUTERS/Rupak De Chowdhuri
Talla

Jami'an agaji sun shafe daren da ya gabata suna kokarin lalubo wadanda suka makale a karkashin gadar yayin da suka bayyana cewa, mawuyaci ne a sake samun wanda ya tsira da ransa.

A jiya Alhamis ne gadar wadda ake ginawa a Kolkata ta fado akan jama'ar da ke hada-hada kamar yadda suka saba yau da kullum, inda ta jikkata mutane kusan 100 baya ga ga kisan da ta yi.
 

To sai dai har yanzu an gaza gano musabbabin rubtawar gadar yayin da jami'an ceto kusan 300 su ka ci gaba da kokarin neman wadanda gadar ta danne duk da cewa an debe tsammanin samun mutun guda da rai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.