Isa ga babban shafi
China

Attajirin China ya ware makudan kudi ga ayyukan agaji

Hamshakin Attajirin China Pony Ma Huateng wanda ya mallaki kamfanin sadarwar na Tencent, yace zai bai wa kungiyoyin agaji hannayen jarinsa da ya kai kudi Dala biliyan biyu.

Shugaban Kamfanin Tencent Pony Ma Huateng
Shugaban Kamfanin Tencent Pony Ma Huateng REUTERS
Talla

Wannan shi ne kyauta mafi girma da wani mutum guda zai bayar a tarihin kasar China.

Pony Ma ya ce bayan ya kwashe shekaru 10 yana bada tallafi ga ayyukan agaji, ya gamsu cewar bada irin wannan kyauta da za ta dauki dogon lokaci ana amfana da ita wajen taimaka gagina al’ummar da ya fito.

Pony Ma dai shi ne a matsayi na 34 cikin attajiran duniya, kuma ya mallaki dukiyar da ta kai sama da Dala biliyan 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.