China ta takaita yin Azumi a Xinjiang
Hukumomi a kasar China, sun haramta wa ma’aikatan gwmanati da Dalibai da masu kananan shekaru yin azumin watan Ramadana musamman a yankin Xinjiang inda ake da musulmi sama da miliyan 10.
Wallafawa ranar:
Sannan gwamnati ta bayar da umurnin bude gidajen abinci a yankin na ‘Yan kabilar Uighur mafi yawancinsu musulmi a lardin Xinjiang.
Ba wannan ne karo na farko ba da hukumomin kasar China ke hanawa musulmin kasar yin azumin watan Ramadana, duk da cewa yin azumin na a matsayin daya daga cikin shikashikan addinin musulunci.
Musulmi na kauracewa Ci da sha da saduwa da iyali a watan Ramadan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu