Isa ga babban shafi
IRAKI

An gano kabari dauke da gawawaki mutane 400 a Fallujah

Sojin Iraki dake yaki don kubutar da birnin Fallujah daga hannun mayakan ISIL sunce sun gano wani kabari dake dauke da gawawakin mutane kusan 400

Gawawakin wasu mutane da aka gano a yankin Sinjar a Iraki
Gawawakin wasu mutane da aka gano a yankin Sinjar a Iraki Reuters/路透社
Talla

Wani jami’in ‘Yan sanda mai mukamin kanar yace an kabarin ne a garin Saqlawiya dake arewa maso yammancin Fallujah.

Jami’in ya kara da cewa cikin gawawakin harda na sojojin gwamnati da kuma fararren hula, kuma akasarinsu an harbe su ne a kai.

Kanar din yace yanzu ana ci gaba da kwashe gawawakin don tantance su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.