Isa ga babban shafi
India

Tsawa ta kashe mutane fiye da 70 a India

Akalla mutane 79 ne suka rasa rayukansu sakamakon wata tsawa da aka yi a jihohin Bihar da Jharkhand da Madhya Pradesh na kasar India.

Ana yawan tafka ruwa kamar da bakin kwarya tsakanin Yuni da Satumba a India
Ana yawan tafka ruwa kamar da bakin kwarya tsakanin Yuni da Satumba a India REUTERS/Stringer
Talla

Hukumomin kasar sun ce, mutane 53 ne suka mutu a Bihar, yayin da 10 suka rasa rayukansu a gabashin jihar Jharkhand, sai kuma mutane 16 da wannan lamari ya yi sanadin ajalisu a Madhya Pradesh.

Rahotanni sun ce, akasarin wadanda suka gamu da ajalinsu na bakin aiki ne a gonakinsu a lokacin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Hukumar adana bayanai kan manyan laifuka ta kasar ta ce, tun daga shekara ta 2005, ake samun mutane dubu 2 a kowacce shekara da ke rasa rayukansu sakamakon tsawa da ake yi a lokacin saukar ruwan sama .

Kashi 80 cikin 100 na ruwan sama a India, na sauka ne a lokacin kakar Monsoon wadda ke fadawa tsakanin Yuni da Satumba na kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.