Isa ga babban shafi
Jordan

Amnesty ta bukaci Jordan ta bude iyakokinta

Kungiyar Kare Hakin Bil Adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin kasar Jordan da ta bude iyakokinta domin karbar ‘Yan gudun hijirar da ke tserewa daga yakin kasar Syria.

Jordan ta haramtawa dubban 'Yan gudun hijirar Syria shiga kasarta
Jordan ta haramtawa dubban 'Yan gudun hijirar Syria shiga kasarta REUTERS/Muhammad Hamed
Talla

Kungiyar tace rufe kofar da kuma hana kai kayan agaji ga dubban ‘yan gudun hijira ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Sarki Abdallah na Jordan ya yi alkawarin daukar mataki mai tsauri bayan harin kunar bakin waken da aka kai wa jami’an tsaron kasar shi akan iyaka a ranar Talata inda aka kashe sojoji 7.

Rundunar Sojin Jordan ta yi zargi kan cewa ‘Yan kunar bakin waken da suka kai harin sun fito ne daga sansanin ‘Yan gudun hijira.

Jordan dai ta karbi dubun dubatar ‘Yan gudun hijirar Syria, kuma har yanzu dubbai ne ke kokarin shiga kasar wadanda suka tagayyara bayan rufe kan iyakokin kasar tun a watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.