Isa ga babban shafi
Pakistan

Harin bam a wani asibiti ya kashe mutane 50

Akalla mutane 50 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashewar wani bam a wani asibiti dake birnin Quetta a kasar Pakistan, kawo yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin na yau litinin da ya jefa kasar cikin jimami.

Harin bam a asibiti dake birnin Quetta ya hallaka mutane fiye da 45
Harin bam a asibiti dake birnin Quetta ya hallaka mutane fiye da 45 REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa yace cikin wadanda suka mutu har da lauyoyi da ‘Yan Jaridu da suka yi gangami dan gudanar da wata zanga zanga saboda kisan gillar da aka yiwa shugaban lauyoyin Balochistan Bilal Anwar Kasi.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa yace cikin wadanda suka mutu har da lauyoyi da Yan Jaridu da suka yi gangami dan gudanar da wata zanga zanga saboda kisan gillar da aka yiwa shugaban lauyoyin yankin Balochistan Bilal Anwar Kasi.

A wani hoton bidiyo da aka yi ta yadawa a shafukan Internet anga gawarwakin jama’a waste a harabar asibitin wasu ma na fidda hayaki wasu kuma jinajina cikin jinni.
Lauyoyi da jami’an kiwon lafiya a asibitin cikin kaduwa sun yi ta kokarin kaiwa mutanen da suka sami rauni doki.

Harin na yau ya kasance hari na biyu mafi muni a wannan shekarar bayan wanda kungiyar Taliban ta dauki alhakin kaiwa a wurin shakatawa dake birnin Lahore da ya hallaka mutane 75.

Firai Minista Nawaz Sharif ya yi tir da Allah wadai da harin na yau da ya auku a yayin gangamin da Lauyoyi suka shirya yi don adawa da kisan Bilal Anwar Kasi da wasu yan bindiga biyu suka yi a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.