Isa ga babban shafi
Myanmar

Musulman Rohingya zasu sami sa’ida

Myanmar ta nada wani kwamitin da zai yi nazari kan halin da al'ummar Rohingya Musulmi ke ciki a kasar domin baiwa gwamnati shawara kan matakan da ya dace a dauka na kawar da cin zarafin 'yan kabilar.

'Yan kabilar Rohingya na fuskantar matsanancin halin kunci a Myanmar
'Yan kabilar Rohingya na fuskantar matsanancin halin kunci a Myanmar REUTERS/Tarmizy Harva/Files
Talla

kwamitin wanda ke karkashin shugabancin tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan zai bada shawara kan yadda za'a warware matsalar da aka samu na yadda ake kallon Yan kabilar Rohingya Musulmi a matsayin wadanda ba 'yan kasa ba da kuma yadda ake musguna musu.

'Yan kabilar Rohingya na fuskantar matsanancin halin kunci, musgunawa, azabtarwa da kuma takaita musu walwala saboda yadda sauran al'ummar kasar ke kallon su a matsayin wadanda suka fito daga wata kasa.

Kungiyoyin kasashen duniya da dama da masu kare hakkin Bil Adama sun dade suna sukar gwamnatin Myanmar kan yadda ake cin zarafin 'yan kabilar ta Rohingya.

Fadar Aung San Suu Kyi ta sanar da cewar kwamitin a karkashin Kofi Annan zai bada shawarwari kan yadda za'a sasanta al'ummar kasar da kuma tallafawa 'yan kabilar Rohingya da kuma bunkasa Yankin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.