Isa ga babban shafi
Turkiyya-Syria-Amurka

Hari kan Kurdawa kuskure ne inji Amurka

Yakin da kasar Turkiya ta kaddamar a makon da ya gabata a yankin arewacin kasar Syria kan mayakan kurdawa da IS, na ci gaba da yin kamari, yayin da Amurka ta bayyana harin na Turkiya da zama babban kuskure.

Iyakar Turkiya da Syria da ake ruwan wuta tsakanin dakarun Sojin kasar da Kurdawa
Iyakar Turkiya da Syria da ake ruwan wuta tsakanin dakarun Sojin kasar da Kurdawa AFP
Talla

Mataimakin Firiministan kasar Turkiya Numan Kurtulmus, ya ce manufar wannan yaki dai shine yunkuri shafe dukkanin wasu kungiyoyin dake ikrarin jihadi na IS, da kuma hana dakarun Kurdawan na PYD samar da mashigi da zai raba kan iyakarta da Syria.

Yanzu haka dai tun bayan kutsen da dakarun kasar Turkiya suka yi a cikin kasar Syria da nufin fatatakar mayakan IS da na kurdawa a makon da ya gabata, lamurra na ci gaba da gurbacewa.

A yau jiragen yakin kasar Turkiya sun ci gaba da ruwan wuta a kan mayakan kurdawa na kungiyar PKK a arewacin kasar Iraki.

Sai dai kuma a daya bangaren ofishin ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagone ya sanar da cewa fadan da ake tafkawa tsakanin dakarun kasar Turkiya da na hadin guiwar larabawa da kurdawa dake samun goyon bayan kasar ta Amurka a Syria ba abin amincewa ba ne.

A cikin wata sanarwa ofisin tsaron na Amurka Pentagon ya ce, yanzu haka ana ci gaba da samun mummunan fada tsakanin dakarun Turkiya da na rundunar FDS dake samun tallafin Amurka, wajen yaki da IS a Syria, bai dace ba kuma babbar barazana ce da ka iya kara jefa yankin cikin mawuyacin hali.

Wannan dai zai kara jefa yar ranke ranken diplomasiyar dake tsakanin Amurka da Turkiya da ta tabarbare sakamakon juyin mulkin da bai cimma nasara ba a Turkiya, da take zargin Fetullah Gulen da shiryawa, wanda kuma ke samun mafaka a kasar ta Amurka a cikin tararrabi bayan da ake ganin sun dan fara samun fahimtar juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.