Isa ga babban shafi
Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta yabi mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Mazauna birnin Aleppo sun ce a karon farko sun kwana cikin nutsuwa ba tare da jin karar bama bamai ko musayar wuta ba sakamakon yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ta kwanaki bakwai.

An samu kwanciyar hankali a Aleppo, a ranar farko ta yarjejeniyar tsagaita wuta
An samu kwanciyar hankali a Aleppo, a ranar farko ta yarjejeniyar tsagaita wuta Reuters
Talla

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Staffan de Mistura yabawa bangarorin da ke rikici a kasar saboda mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sai dai Staffan De Mistura ya bayyana damuwa bisa rashin fara kai kayayyakin agaji da suka hadarda magunguna da abincida ake fatan yi.

De Mistura ya musanta rahoton da wata kafar yada labaran Turkiya da ya ce motocin Majalisar Dinkin Duniya dauke da kayan abinci sun fara shiga kasar Syria danufin mika kayan agaji.

Sai dai kuma ya ce tuni Majalisar Dinkin Duniyar a shirye ta ke don tura tawagarta cikin kasar.

Sama da mutane 300,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin na Syria wanda ya barke a shekara ta 2011.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.