Isa ga babban shafi
Philippines

Philippines ta bukaci ficewar sojojin Amurka daga kasar

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte ya bukaci ficewar wata rundunar Amurka ta musamman ta sojojin ruwa daga tsibirin Mindanao da ke kudancin kasar.

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte
Shugaban Philippines Rodrigo Duterte REUTERS/Lean Daval Jr
Talla

A cewar Duterte muddin sojojin kasar Amurkan suka cigaba da zama a tsibirin na Mindanao ba za’a samu zaman lafiya ba a yankin.

Rundunar sojin ruwan Amurkan dai ta shafe sama da shekaru 20 a tsibirin bisa amincewar dokar kasar a waccan lokaci.

Shugaban na Philippines ya bukaci ficewar sojojin, kwanaki kadan bayan da ya ce zai sauya manufofin kasar a kasashen ketare musamman kan kasar Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.