Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta zargi Rasha da aikata rashin tausayi a Aleppo

Wakiliyar kasar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, ta zargi kasar Rasha da aikata rashin tausayi dangane da jagorantar luguden wuta da take yi a birnin Aleppo a Syria. 

Sojoji da suke biyayya ga shugaban Syria Bashar al-Assad dauke da tutar kasar bayan kwace kudu maso yammacin birnin Aleppo daga hannun 'yan tawaye a ranar Lahadi
Sojoji da suke biyayya ga shugaban Syria Bashar al-Assad dauke da tutar kasar bayan kwace kudu maso yammacin birnin Aleppo daga hannun 'yan tawaye a ranar Lahadi SANA/Handout via REUTERS
Talla

Samantha Power ta bayyana haka ne yayin gudanar da taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, inda ta ce duk bayanan da Rasha take fitarwa kan rawar da take takawa a Syria zunzurutun karya ce.

Yayin da Power ke wannan jawabi ga zauren Majalisar, wakilin kasar Rasha  Vitaly Churkin bai musanta rawara da kasarsa ke takawa ba kan fadan da ke gudana a birnin Aleppo.

Sai dai Churkin ya zargi bangaren ‘yan tawayen Syria da yin zagon kasa ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma.

Churkin ya kara da cewa zai yi wahala a kawo karshen yakin da Syria ke fuskanta a yanzu, yayinda sojojin gwamnatin Syria suka kara zafafa kai hari kan yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawayen kasar a birnin Aleppo.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.