Isa ga babban shafi
India

India ta rattaba hannu kan yarjejeniyar dumamar yanayi

Kasar India ta rattaba hannu kan yarjejeniyar dimamar yanayi da aka cimma a birnin Paris na Faransa da zummar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a duniya.

Firaministan India Narendra Modi
Firaministan India Narendra Modi REUTERS/Etienne Oliveau/Pool
Talla

Kasar wadda ita ce ta uku wajen fitar da hayakin, ta rattaba hannun ne yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Mahatma Ghandi.

A jiya Lahadi, India ta rattaba hannu kan yarjejeniyar, a dai dai lokacin da ta ke bikin tunawa da tsohon jagoranta da ya taimaka wajen samun yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka, Mahatma Ghandi.

Kasar mai yawan al’umma biliyan 1 da miliyan 300, ita ce ta baya-bayannan daga cikin kasashen duniya da suka fi gurbata muhalli da ta rattaba hannun, abin da ake ganin zai taka rawa wajen kawo karshen dumamar yanayin a duniya.

Dama dai Firaministan India Nerandra Modi ya ce, a ranar 2 ga watan Oktoba, da ta kasance ranar hutu ga ilahirin al’ummar kasar, za su rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Ministan muhallin kasar, Anil Madhav Dave ya ce, tun a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York na Amurka, suka gabatar da tsarinsu na rattaba hannun.

Yarjejeniyar dai ta bukaci kasashen duniya 55 da ke fitar da kashi 55 na hayaki mai guba da su zartar da ita, yayin da Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon ya bayyana kwarin gwiwar cewa, yarjejeniyar za ta fara aiki nan da karshen shekarar da muke ciki.

Tuni Amurka da China suka rattaba nasu hannun yayin da a cikin makon jiya, ministocin muhalli na kasashen Turai suka amince cewa, suma za su gagaguta rattaba hannu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.