Isa ga babban shafi
Yemen

HRW ta ce Saudia na aikata laifukan Yaki a Yemen

Kungiyar kare hakkin biladama ta, Human Right Watch, ta bayyana harin sama da ya lakume rayukan mutane 140 da ke zaman makoki a Yemen, a matsayin laifukan Yaki, inda ta bukaci a sanyawa Saudi Arabia takukumin sayar mata da makamai.

Saudi na ci gaba da kai munanan hare-hare a Yemen
Saudi na ci gaba da kai munanan hare-hare a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Harin na Assabar din makon da ya gabata, an daura alhakinsa kan rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta, kuma ya kasance mafi muni da rundunar ke kai wa kan ‘yan tawaye da kawayansu.

A cewar HRW, harin kan masu zaman makoki, na bukatar binciken gaggawa mai inganci daga kasashen duniya, domin ya bayyana irin rashin imani da kashe fararan hula da gan-gan.

Kungiyar ta kuma bukaci manyan kasashen duniya da suka hada da Amurka da Britaniya da su gaggauta daina sayarwa Saudiya makamai.

HRW, ta ce bayan hare-hare rashin imani kan makaranatu da kasuwa da asibitoci da taron bikin tsawon watanni 19 a Yemen, rundunar kawance Saudiya yanzu ta sanya masu zaman makoki cikin jerin wadanda za ta duga hallakawa.

Daga cikin wadanda aka rawaito an hallaka a harin na baya-baya nan hada wani jigon ‘yan tawayen kasar Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.