Isa ga babban shafi
Iraq

Iraqi ta yi watsi da tayin Turkiya na murkushe ISIL a Mosul

Firaministan Iraqi Haidar al-Abadi yaki amincewa da tayin Turkiya na bada taimakon sojinta domin murkushe mayakan ISIL da ke birnin Mosul.

Firaministan Iraqi Haidar al Abadi
Firaministan Iraqi Haidar al Abadi
Talla

A cewar al Abadi, sojin Iraqi na da karfin kakkabe mayakan na ISIL ba tare da taimakon Turkiya ba.

Turkiya ta gabatar da wannan bukata, bayan ziyarar da Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ya kai kasar, inda ya ce Turkiya zata iya bada gudunmawa don kawo karshen mayakan na ISIL.

An dai fara samun takun saka, tsakanin Turkiya da Iraqi bayan da Firaminista Haidar al Abadi ya bukaci janyewar sojin Turkiya daga garin Bashiqa, da kusa da Mosul inda suke horar da sojin Iraqi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.