Isa ga babban shafi
Falasdinawa

Na san wanda ya kashe Arafat- Abbas

A yayin da ake tunawa da Yasser Arafat da aka kashe tsawon shekaru 12 a yau, shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya ce ya san wanda ya kashe tsohon shugaban amma ba tare da ya fadin suna ba.

Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat
Tsohon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat REUTERS/Suhaib Salem/Files
Talla

Da ya ke jawabi a gaban dubban Falasdinawa a Ramallah, Shugaba Abbas ya ce idan aka tambaye shi wa ya kashe Arafat ya sani amma shaidar shi kadai ba ta isa ba.

Abbas ya ce hukumar da aka kafa domin binciken kisan tana bin diddigi kuma Falasdinawa za su yi mamaki idan suka ji wanda ya aikata kisan.

“Ba na son ambatar sunaye, domin sunaye ne da ba su cancanci a tuna ba” a cewar shugaban na Falasdinawa.

Yaseer Arafat ya rasu ne a wata asibitin Paris a ranar 11 ga watan Nuwamban 2004, ba tare da gano musabbabin mutuwar shi ba.

Falasdinawa sun dade suna zargin Isra’ila ce ta kashe shi ta hanyar guba, zargin da Isra’ila ke musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.