Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta dauki alhakin tada bam a cibiyar soji mafi girma

Jami’an Rundunar Tsaro ta NATO, dana Afganistan sun tabbatar da fashewar bam a cibiyar Sojin Amurka mafi girma a kasar da sanyin safiyar yau.

Wasu jami'an tsaron Afghanistan da ke filin jiragen sama na Bagram.
Wasu jami'an tsaron Afghanistan da ke filin jiragen sama na Bagram. REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Kamfannin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewar, mutane 3 suka rasa rayukansu, yayinda swasu 13 suka samu munanan raunuka a yankin Bagram inda cibiyar sojin ta ke.

Yanzu haka Amurka na da jimillar sojoji 10,000 a Afghanistan, inda bataliya mafi girma ke Bargram.

Jim kadan bayan kai harin kakakin kungiyar Taliban Zabinullah Mujahid ta shafinsa ba Twitter, ya sanar da cewa sune suka kai harin.

Ko a baya, cibiyar sojin mafi girma da ke makeken filin jiragen sama na Bagram ta sha fama da hare haren 'yan kungiyar Taliban, tun bayan kawo karshen ayyukan samar da tsaro a Afghanistan da kungiyar tsaro ta NATO ta yi, shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.