Isa ga babban shafi
Syria-Faransa

Sabon tattaunawa kan rikicin Syria

Kasar Faransa ta ce kasashen da ke goyan bayan 'yan adawar Syria za su gudanar da wani taro a birnin Paris farkon watan gobe a ci gaba da lalubo hanyar magance rikicin kasar da yaki ci yaki cinyewa.

Kasashen da ke tattauna rikicin Syria
Kasashen da ke tattauna rikicin Syria Reuters
Talla

Faransa ta kuma bukaci daukar mataki kan Syria da kawayen ta da ke amfani da makami mai guba kan fararen hula.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault ya bayyana shirin gudanar da taron inda ya ke cewa cikin kasashen da zasu halarci taron harda kasar Amurka da wakilan kasashen da ke Yankin teku.

Ministan ya ce ya da ce kasashen duniya su dai na kauda kan su kan irin ta’addancin da ake aikatawa a Syria yanzu haka.

Ayrault ya ce ya zama dole su dauki mataki kan abin da ke faruwa yanzu haka na kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba.

Yanzu haka dakarun d ake goyan bayan shugaba Bashar al Assad na ci gaba da kutsawa birnin Aleppo a kokarin karbe birnin daga mayakan ISIS.

Kasashen da za su halarci taron sun hada Amurka da Jamsu da Faransa da Italiya da Birtaniya.

Sauran sun hada da Saudi Arabia da Qatar da Daular Larabawa da kuma Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.