Isa ga babban shafi
Syria

Dakarun Syria na yakar ‘Yan tawaye a Aleppo

Dakarun gwamnatin Syria na ci gaba da yakar ‘Yan tawaye a garin Aleppo domin kwato ikon garin. Wannan na zuwa bayan wani rahoto da ya ce a cikin sa’oi 72 mutane sama da 20,000 suka tserewa gidajensu daga yankunan garin da ‘Yan tawaye suka kwace iko tun a 2012.

Dakarun Syria sun kwace gabashin Aleppo daga hannun 'Yan tawaye
Dakarun Syria sun kwace gabashin Aleppo daga hannun 'Yan tawaye REUTERS/Rodi Said
Talla

Kasar Faransa ta kira wani taron Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na gaggawa don nazari kan halin da fararen hula ke ciki a Aleppo na kasar Syria.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Francois Delattre ya ce kasar da kawayenta ba za su rufe idonsu kan abin da ya kira kisan kiyahsin da ake yi wa fararen hula, wanda shi ne mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu.

Jakadan Birtaniya Matthew Rycroft ya ce abin takaici ne irin halin kunci da mutanen Aleppo suka samu kan su.

Dakarun gwamnatin Syria sun kwashe kusan watanni hudu da yi wa birnin kawanya wajen ganin sun murkushe ‘Yan tawayen da suke rike da birnin tun 2012.

Jakadan Birtaniya ya ce makomar Aleppo yana hannun gwamnatin Syria da kuma Rasha, inda ya bukaci bangarorin biyu su kawo karshen ruwan wutar da suke a birnin.

‘Yan tawayen Syria dai na smaun taimako ne daga kasashen yammaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.