Syria
IS ta sake shiga birnin Palmyra na Syria
Mayakan kungiyar IS sun sake shiga birnin Palmyra wanda da dakarun Syria suka fatattake su daga cikinsa watanni takwas da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Talla
Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta ce, a halin yanzu mayakan sun mamaye yankin arewa maso yammacin birnin, in da kuma suke gwabza yaki da sojojin gwamnati.
Birnin dai ya shafe kusan shekara guda a hannun mayakan kafin kwace shi a cikin watan Maris.
Rahotanni sun ce, tuni fararen hula suka fara tururuwan ficewa daga birnin mai dimbin tarihi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu