Isa ga babban shafi
Philippines

An kashe shugaban masu da’awar Jihadi a Philippine

Jami’an tsaro a Philippine sun ce sun kashe babban kwamandan kungiyar masu tsatstsauran ra’ayin Islama da ke kisan mutane domin samun goyon bayan kungiyar IS da ke da’awar jihadi a Iraqi da Syria.

Jami'an tsaron Philippine sun dade suna farautar Jaafar Maguid da suke nema ruwa a jallo
Jami'an tsaron Philippine sun dade suna farautar Jaafar Maguid da suke nema ruwa a jallo REUTERS/Stringer
Talla

‘Yan sandan Philippine sun ce an harbe Mohammad Jaafar Maguid ne a Mindanao kusa da gabar teku a tsakiyar dare a jiya tare da cafke wasu mayakansa.

Jaafar Maguid shi ne jagoran kuungiyar ‘Yan ta’adda da ake kira Ansarul Khilafa da ta salwantar da rayukan mutane sama da 120,000.

Maguid da Jami’an tsaron Philippine ke nema ruwa a jallo, na jagorantar hare haren bama bamai yawanci a gangamin jama’a.

Sannan rundunar ‘Yan sanda Philippine ta ce mayakan na amfani ne da tutar IS da suka kafa a sansanoninsu domin neman samun goyon kungiyar da ke da’awar jihadi a Syria da Iraqi.

Bayan tabbatar da kashe Maguid, Jami’an tsaron Philippines sun yi gargadin daukar matakan shirin ko-ta-kwana domin kare hare haren daukar fansan daga mayakan kwamandan na Ansaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.