Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Rasha ta fara janye dakarunta daga Syria

Rasha ta fara rage dakarunta hadi da yawan makaman yakinta a Syria, musamman manyan jiragen yakinta da ta jibge da ke taimakawa dakarun Bashar Al Assad wajen yakar ‘Yan tawaye.

Daya daga cikin jiragen yakin Rasha a Syria
Daya daga cikin jiragen yakin Rasha a Syria
Talla

A cewar rundunar sojin Rasha, jiragen yakin sun kammala aikin da aka tura su yi a Syria.

Babban hafsan sojin Rasha Valery Gerasimov ne ya sanar da matakin janye makaman sojin a Syria kamar yadda babban kwamandan sojin kasar kuma shugaban kasa Vladimir Putin ya bukata.

Taimakon sojin Rasha da suka shiga Syria a watan satumban 2015, ya taimakawa dakarun Assad yakar ‘yan tawaye tare da kawato birnin Aleppo.

Jiragen dai sun kai farmaki 420 tare da kai hare hare a waurare 1,252 na maboyar ‘yan twayen Syria cikin watanni biyu.

Sai dai kuma, har yanzu Rasha tace tana da sauran karfin soji a Syria

Masu sharhi dai na ganin fara ficewar makaman yakin na Rasha zai taimakawa kokarin sulhun da kasar ke yi tsakaninta da ‘yan tawayen bisa jagorancin Turkiya, Iran da ita kanta Rasha na kawo karshen rikicin kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.