Mutane 7 sun mutu a zanga-zangar kin jinin gwamnati
Akalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu ciki har da Dansanda guda a arangamar tsakanin masu zanga-zangar neman gudanar da sauye sauye a hukumar da ke sa ido kan lamurran zabuka da jami’an tsaro a birnin Baghdad na Iraki.
Wallafawa ranar:
Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zangar a yau asabar, baya ga wadanda suka mutu akwai wasu da dama da suka sami rauni kamar yadda wani babban jami’in ‘yansandan kasar ya sanar.
Rahotanni na cewa an jefa wasu rokoki a yankin tsaro na Green zone da ake da ginin majalisar dokokin kasar da ofisoshin jakadancin wasu kasashen Duniya.
Al’amarin ya auku ne a tsakiyar birnin Baghdad.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu