Yar jarida ta mutu a farmakin kwato Mosul
Rahotanni daga kasar Iraki na cewa wata ‘yar jarida ta rasa ranta a lokacin da take kokarin dauko rahoto a fadan da ake yi a tsakanin gwamnatin Iraki da mayakan Daesh na ISIL na sake kwato birnin Mosul.
Wallafawa ranar:
Kafar talabijin Kurdawan Iraki da ‘yar jaridar ke aiki ce ta sanar da mutuwarta.
‘Yar jaridar mai suna Shifa Gardi ta gamu da ajalinta a harin bam a yau asabar.
Ta kuma mutu ne tana da shekaru 30 a Duniya.
A makon da ya gabata ne dakarun sojin Iraki suka kaddamar da farmakin sake kwato birnin Mosul birni na biyu mafi girma a kasar daga ikon mayakan ISIL.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu