An kashe fararen hula da dama a Mosul
An kashe fararen hula da dama a Mosul a luguden wutar da jiragen Iraqi da na Amurka ke yi ta sama kan mayakan IS. Rahotanni sun ce daruruwan mutane ne ke tserewa daga Mosul
Wallafawa ranar:
Gwamnan lardin Nineveh Nawfal Hammadi inda Mosul ne babbar birnin lardin, ya ce hare haren jiragen sama na Iraqi da Amurka da kawayenta suka kai a Mosul ya kashe fararen hula sama da 130. Kuma sun lalata gidaje sama da 27.
Rahotanni sun ce rayuwan dubban fararen hula na cikin hatsari a yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun Iraqi da mayakan IS.
Amurka ta amsa jiragen yakinta sun kai hari a inda aka kashe fararen hula a Mosul.
An dade dai dakarun Iraqi na kokarin kwarto Mosul daga hannun mayakan IS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu