Isa ga babban shafi
Syria

An mutunta Tsagaita buda wuta a kudancin Syria

Ana sa ran wakilan Gwamnatin kasar Syria da ‘Yan Tawaye za su sake haduwa a teburin tattaunawa a Geneva karo na bakwai da zummar kawo karshen rikicin kasar a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

An tsagaita wutar ne a yankin Daraa da Quneitra da Sweida a kudancin Syria
An tsagaita wutar ne a yankin Daraa da Quneitra da Sweida a kudancin Syria REUTERS/Alaa Al-Faqir
Talla

Taron na zuwa ne bayan kasashen Amurka da Rasha da Jordan sun sanar da kulla wata yarjejeniyar tsagaita wuta a Kudancin Syria. Kuma rahotanni sun ce bangarorin biyu sun mutunta yarjejeniyar.

Irin wannan taron da aka yi a watan Mayu ya watse ba tare da samun nasara ba, a yakin da tuni ya lakume rayukan mutane sama da 320,000 tun bayan barkewarsa a watan Maris na shekarar 2011.

Manyan batutuwan da ake sa ran taron zai duba sun hada da rubutawa kasar sabon kundin tsarin mulki da yadda za a tafiyar da mulkin kasar da zabubbukan da za a yi da kuma yaki da ta’addanci.

‘Yan adawar kasar sun kekashe kasa cewar dole sai shugaba Bashar Al Assad ya sauka daga kujerarsa, yayin da bangaren Gwamnati ke yin watsi da matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.