Isa ga babban shafi
Gulf

Kasashen tekun Fasha sun soma sassautawa Qatar

Manyan Kasashe hudu na tekun fasha sun sassauta yawan bukatun da suka shatawa Qatar daga 13 zuwa guda 6 domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.

Kasashe hudu na tekun fasha sun sassauta yawan bukatun da suka shatawa Qatar
Kasashe hudu na tekun fasha sun sassauta yawan bukatun da suka shatawa Qatar REUTERS/Khaled Elfiqi
Talla

Tun da farko dai Qatar ta ki amincewa da dukkanin bukatun kasashen na Larabawa da suka hada da rufe tashar talabijin ta Aljazeera.

Saudiya da Masar da Daular larabawa da Bahrain sun amince su sassauta bukatun zuwa 6 daga 13 da suka gindayawa Qatar tun da farko, kamar yadda wakilansu a Majalisar Dinkin Duniya suka tabbatarwa manema labarai.

Daga cikin bukatun da har yanzu kasashen ke son Qatar da amince sun hada alkawarin yakar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi da kuma kawo karshen duk wani mataki na tunzarawa da tsokanar juna.

Kuma wakilan kasashen sun ce an sassauta sharuddan ne saboda suna son a kawo karshen rikicin tsakaninsu da Qatar.

Sai dai Zuwa yanzu babu martani daga bangaren Qatar da tuni ta yi watsi da da sharudan 13 da kasashen suka shata makwanni 6 da suka gabata.

Manyan bukatun kasashen dai sun hada rufe kafar yada labaran Aljazeera mallakin Qatar da rufe sansanin Turkiya da katse hulda da kungiyar ‘yan uwa musulmi da rusa duk wata hulda da Iran.

Kuma ga alamu kasashen yanzu sun yi watsi da batun rufe tashar Aljazeera daga cikin bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.