Isa ga babban shafi
India

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 200 a India

Mutane sama da 200 sun rasa rayukansu samakon ambaliyar ruwa da ta auku bayan tafka mamakon ruwan sama mai tafe da iska a yammacin India kamar yadda masu aikin agaji suka tabbatar.

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200 a India
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200 a India Reuters
Talla

Alkaluman mamata a jihar Gujarat sun karu kan wadanda aka bayar a makon  jiya na mutuwar mutane 123, bayan masu aikin ceto sun kutsa yankunan da ibtila'in ya shafa, musamman a karkara.

A cewar daraktan hukumar agajin gaggawa ta jihar, A.J Shah, sun samu damar kwashe gawarwaki 213, yayin da ake ci gaba da tantance wasu daban.

Kamfanin Dilancin Labaran Faransa na AFP, ya rawaito wani jami’in agaji da ya bukaci a sakaya sunansa na cewa, ana jan kafa wajen aiwatar da gwajin da ake yi wa wasu gawarwakin.

Rahotanni sun bayyana cewa, cikin wadanda aka tsinto gawarwakinsu, har da iyalai ‘yan gida daya su 17 a wani kauye mai suna Banaskantha da ke garin na Gujarat.

Yanzu dai akwai mutane 130 da aka gano da sauran numfashi, kana ana ci gaba da amfani da jirage masu saukan angulu da kwale-kwale wajen kai agaji ga wadanda suka makale a sanadiyar ambaliyar.

Firaministan India Nerandra Modi, da shi ma ya tsallake rijiya da baya a lokacin da ya ke gabatar da wani shiri a wata tashar rediyo da ke Gujarat, ya ce wadanda ambaliyar ruwan ta shafa za su samu agajin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.