ISIS ta kai hari a ofishin jakadancin Iraqi a Afghanistan
Jami’an tsaron Afghanistan na dauki-ba-dadi da mayakan ISIS a harabar ofishin jakadancin Iraqi da ke birnin Kabul
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayan wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a kofar shiga harabar ofishin jakadancin, yayin da wasu mayaka uku suka yi nasarar kutsawa cikin harabar.
Kawo yanzu babu wani bayani game da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata a harin na yau.
An dai kwahe ma’aikatan ofishin jakadancin bayan jami’an tsaron sun kai dauki kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan ta sanar.
Bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya a binin na Kabul, yayin da ake ci gaba da jin karar jiniyar motocin dauka marasa lafiya da kuma harbe-harben bindiga.
‘Yan ta’adda da suka hada da Taliban sun kai hare-hare da dama a Afghanistan a cikin wannan shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu