Isa ga babban shafi
Iraqi

Sojin Iraqi sun kaddamar da farmakin kwato Tal Afar daga IS

Rundunar sojin Iraqi mai samun goyon bayan Amurka, ta kaddamar da farmakin kwato garin Tal Afa, wanda har yanzu ya ke hannun mayakan IS.

Tankar yakin sojin Iraqi, yayinda suka kaddamar da farmaki kan mayakan IS.
Tankar yakin sojin Iraqi, yayinda suka kaddamar da farmaki kan mayakan IS. REUTERS
Talla

Tun a watan yulin da ya gabata ne dai sojin Iraqi, mayakan sa kai na Kurdawan Peshmerga da na mabiya Shi’a suka yiwa garin na Tal Afar kawanya, wanda ke da nisan kilomita 80 yamma da birnin Mosul.

Kwamandojin sojin Amurka da na Iraqi, sun ce akwai kimanin mayakan kungiyar ta IS 2000, da har yanzu ke cikin garin, wadanda ake sa ran zasu yi mummunar turjiya, duk da cewa wata kwakkwarar majiya ta rawaito, mayakan suna fuskantar karancin abinci da ma kayan fada, bayan shafe tsawon lokci jiragen yaki na musu luguden wuta.

Kafin kaddamar da farmakin sojin Iraqi sun yi jefa sanarwa ga fararen hula da su dauki matakan kare kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.