Isa ga babban shafi
Philippines

Philippines: Mutane sun fara fusata da salon yakar miyagun kwayoyi

Dubban mutane ne suka shiga wata zanga zangar da akayi a Manilla, babban birnin kasar Philippines, domin nuna rashin amincewa da yaki da masu safarar miyagun kwayoyin da shugaba Rodrigo Duterte ke yi, bayan kashe wani matashi.

'Yan uwa ga Leover Miranda, matashin da jami'an tsaron kasar Philipinnes suka hallaka, bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, hakan yasa wasu dubban mutanen fitowa domin gudanar da zanga-zanga.
'Yan uwa ga Leover Miranda, matashin da jami'an tsaron kasar Philipinnes suka hallaka, bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, hakan yasa wasu dubban mutanen fitowa domin gudanar da zanga-zanga. REUTERS/Romeo Ranoco
Talla

A lokacin da akayi jana’izarsa ajiya, majiyoyi masu tushe sun rawaito cewa babu abinda ya hada matashin mai suna Leover Miranda, da mu’amala da miyagun kwayoyin.

Mahaifin Miranda ya bukaci abi masa hakkin dan sa da aka kashe.

A gefe guda kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun ce kashi biyu bisa uku na mutanen kasar ta Philipinnes sama da 3,500 da aka kashe, babu abinda ya hada su da kwaya.

Ko a makon da ya gabata kadai, sai da ‘yan sanda kasar suka hallaka akalla mutane 80 da suka ce masu safara ne ko kuma tu’ammuli da miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.