Isa ga babban shafi
Afghanistan

Trump ya bayyana shirin girke karin sojoji 4,000 a Afghanistan

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin girke karin sojoji 4,000 a Afghanistan sabanin shirin sa na janye dakarun Amurka daga kasar, yayin da ya zargi Pakistan da bai wa mayakan Taliban mafaka a cikin kasar ta.

Donald Trump ya yi watsi da sukar da ake masa na cewar yaki asara ne wajen bata lokaci da kudi
Donald Trump ya yi watsi da sukar da ake masa na cewar yaki asara ne wajen bata lokaci da kudi REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Trump ya kuma ce ta hanyar tattaunawa ne kawai za a iya magance rikicin Afghanistan baki daya amma ba ta hanyar soji ba.

A jawabin sa na farko ga Amurkawa tun hawan sa karagar mulki, shugaba Donald Trump ya yi watsi da sukar da ake masa na cewar yakin asara ne wajen bata lokaci da kudi, inda ya ke cewa matsalar ba kamar yadda Amurkawa ke kallon ta daga waje bane.

Trump ya ce bukatar sa ita ce janyewa daga yakin Afghansitan wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban Amurkawa da kuma lakume biliyoyin daloli, amma bayan watanni ana tatatunawa ficewa daga kasar zai bai wa 'yan ta’adda damar samun wurin zama.

Shugaban bai bayyana adadin sojin da zai sake turawa kasar ba, amma jami’an sa sun ce tuni ya amince da a tura 3,900 kari kan wadanda ke kasar.

Shugaban ya soki Pakistan wanda ya ce duk da biliyoyin dalolin da Amurka ke basu, kasar na samar da mafaka ga mayakan Taliban, yayin da ya ke cewa watakila nan gaba a tattauna da kungiyar domin kulla yarjejeniyar siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.