Isa ga babban shafi
Myanmar

Sabon rikici ya yi sanadi rayuka 89 a Myanmar

Akalla mutane 89 suka mutu cikin su harda jami’an tsaro a wani hari da ‘yan tawayen Myanmar suka kai wa jami’an tsaron kwantar bauna a Jihar Rakhine.

Sabon rikici ya yi sanadi rayuka a Myanmar
Sabon rikici ya yi sanadi rayuka a Myanmar Reuters
Talla

Kwamandan sojin Yankin Min Aung Hlaing ya ce cikin wadanda suka mutu harda soja guda da ‘yan Sanda 10, sai kuma mahara 77

Harin na wannan juma’a na zuwa ne kwana guda bayan gabatar da rahotan kwamitin binciken Kofi Annnan wanda ya bukaci gwamnatin kasar ta janye dokar takaita zirga zirgar Yan kabilar Rohingya Musulmi.

A cikin shekarar bara ne shugabar gwamnatin Myanmar An San Suu Kyi ta nada Kofi Annan domin ya jagoranci wannan bincike, inda ta yi alkawarin cewa gwamnati za ta amince da illahirin abubuwan da kwamitin zai gano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.