Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Nukiliya: Kasashen duniya sun maida martani kan Korea ta Arewa

Kasashen duniya sun mayar da martani kan gwajin makamin Nukiliya da Korea Ta Arewa ta yi a karo na shida, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiyar yankin.

Hoton da kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa (KCNA)  ya wallafa, da ke nuna yadda kasar ta yi gwajin makami mai linzami a rabar 9 ga Agustan 2017.
Hoton da kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa (KCNA) ya wallafa, da ke nuna yadda kasar ta yi gwajin makami mai linzami a rabar 9 ga Agustan 2017. STR / KCNA VIA KNS / AFP
Talla

Tuni Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, kasarsa na duba yiwuwar katse huldar kasuwanci da duk kasashen duniya da ke da alakar cinikayya da Korea ta Arewa.

Trump ya kuma nanata cewa, China na da damar dakatar da makwabciyarta daga shirinta na makaman nukiliya.

Su kuwa kasashen Jamus da Faransa da Italiya duk sun bukaci kungiyar kasashen Turai da ta sanya takunkumai masu tsauri kan Korea ta Arewa bayan abin da suka kira sabuwar takalar fada da ta yi.

A zantawar da suka yi ta wayar tarho, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron sun amince cewa, Korea ta Arewa ta wuce giona da iri, domin ta keta dokokin kasa da kasa, saboda haka ya dace a dauki kwakkwaran mataki.

Ita ma Japan cewa ta yi, lallai sabon gwajin wanda shi ne karo na shida da Korea ta yi a ‘yan kwanakin nan, ba abin a kawar da kai bane.

Sai dai shugaban Rasha Vladmir Putin, ya bukaci kwantar da hankula, inda ya ce, ta hanyar siyasa da diflomasiya ne za a iya magance wannan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.