An yi zanga-zangar goyon bayan Musulman Myanmar
Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Pakistan da Malaysia a yau Juma’a domin nuna adawa da kisan Musulmin Rohingya a Myanmar wadanda ke ci gaba da tserewa zuwa Bangladesh.
Wallafawa ranar:
Masu zanga-zangar sun fito suna daga kwali mai dauke da sakon da ke alla-wadai da shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
Suu Kyi da ta samu lambar yabo ta zaman lafiya a duniya na ci gaba fuskantar suka kan yadda ta ki fitowa fili ta soki yadda ake kisan mutanen na Rohingya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane 1000 jami’an tsaron Myanmar suka kashe, yayin da sama da dubu dari uku suka fice zuwa Bangladesh don neman mafaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu