Isa ga babban shafi
Iran

'Kazafin da Amurka ke yi mana ya isa haka'

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei, yace kasar ba zata baiwa Amurka kai bori ya hau ba, dangane da yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da manyan kasashen duniya.

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei.
Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei. REUTERS/Handout
Talla

Yayin jawabi ga al’ummar kasar, Ayatollah yace Iran kasa ce mai karfi kuma ba zata lamunce duk wata barazana daga gwamnatin Amurka ba, wadda ta bayyana ta a matsayin makaryaciya kuma mai yaudara.

Shugaban yace Iran ta mutunta yarjejeniyar da ta kulla, kuma kasashen duniya sun tabbatar da haka, amma Amurka na ci gaba da yiwa kasar kazafi.

Ana saran shugaba Hassan Rouhani ya tattauna kan shirin a taron Majalisar Dinkin Duniya da ake farawa yau a New York.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.