Isa ga babban shafi
Myanmar

Mutanen Rohingya ba ‘yan kasa bane – Sojin Myanmar

Rundunar sojin Myanmar ta bukaci hadin-kan al’ummar kasar wajen bayyana wa duniya ainihin tushen ‘yan kabilar Rohingya.

Wasu 'yan kabilar Rohingya, yayinda ake raba musu abinci a garin Cox's Bazar, na Bangladesh, ranar 16 ga Satumba, 2017.
Wasu 'yan kabilar Rohingya, yayinda ake raba musu abinci a garin Cox's Bazar, na Bangladesh, ranar 16 ga Satumba, 2017. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Rundunar ta ce, mutanen Rohingya ba su da asali a kasar, kuma tana kai mu su hari ne don kakkabe masu dauke makamai da ke cikinsu wadanda ta kira da ‘yan tawaye.

Rundunar Sojin Myanmar ta bayyana cewa, tana kaddamar da hare-haren ne a yankin arewacin jihar Rakhine da zimmar kakkabe ‘yan tawayen na Rohingya karkashin kungiyar ARSA, da suka kai wa jami’an ‘yan sanda hari a ranar 25 ga watan Agustan da ya gabata, lamarin da ya rura tashin hankalin na baya-bayan nan.

Rikicin dai ya tilastawa mutanen Rohingya kimanin dubu 400 neman mafaka a Bangladesh, wadanda suka gujewa kisan gillar a sojoji ke musu da sunan farautar masu dauke da makamai, inda suke kone gidaje hadi da yiwa mata fyade bayaga sauran nau’o’in cin zarafin da gwamnatin kasar ta Myanmar ke cigaba da musantawa.

Rahotanni da hukumomin Bangladesh suka samu na cewa, sojojin Myanmar na yi wa fararen hula a jihar Rakhine yankar rago tare da kona gidajensu.

A gefe guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kisan a matsayin yunkurin share wata al’umma daga doron-kasa.

Akasarin ‘yan asalin Myammar mabiya addinin Bhudda, na kallon ‘yan kabilar Rohingya tamkar baki da suka tsallako daga kasar waje, kuma ba su amince da sunan da ake kiran su na Rohingya ba, in da suka ce hakikanin sunansu shi ne Bengali.

Babban hafsan sojin kasar, Janar Min Aug Hlaing, ya ce, ‘yan kabilar Rohingya sun bukaci Myanmar ta amince da kabilarsu a hukamance bayan sanin kowa ne cewa, babu wata kabila mai wannan suna da ke da tushe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.