Isa ga babban shafi
Iraqi

Kurdawa sun jefa kuri’ar neman samun ‘yancin Kai

Kurdawan Iraqi sun gudanar da kuri’ar raba gardama ta ballewa daga kasar domin samun ‘yancin kai a yau Litinin. Kurdawan sun bijerewa dukkanin wata barazana da gargadi daga Iraqi da Iran da kuma Turkiya da ke adawa da matakin gudanar da kuri’ar.

Kurdawa na jefa kuri'ar ballewa daga Iraqi
Kurdawa na jefa kuri'ar ballewa daga Iraqi REUTERS/Ako Rasheed
Talla

Dubban Kurdawa ne suka jefa kuri’ar da za ta ba su damar ballewa daga Iraqi domin samun ‘yancin gashin kai.

Kurdawan sun yi shiga sanye da tutarsu mai launin ja da fari da kore da kuma doruwa tare da kawata unguwanni da tutar a sassan arewacin Iraqi da suke fatar samun ‘yanci.

Kurdawan sun jefa kuri’ar duk da gargadi daga gwamnatin Iraqi da kuma barazanar takunkumi daga Turkiya da Iran da ke makawabta da su.

Sannan Amurka da kasashen Turai na ganin kuri’ar Kurdawan zai haifar da cikas ga yaki da mayakan IS musamman wargajewar hadin kan da aka samu tsakanin Iraqi da Kurdawan.

Tuni dai Turkiya ta ce za ta rufe kan iyakarta da yankin na Kurdawa tare da hana su fitar da mai.

Kabilar Kurdawa ne na hudu a yawan jama’a a yankin gabas ta tsakiya kuma har yanzu ba su da wata kasa mai cin gashin kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.