Isa ga babban shafi
Iraqi

Kurdawan Iraqi na bikin murnar kada kuri'ar raba gardama

Kurdawan Iraqi sun shafe daren jiya suna murnar nasarar da suka samu na gudanar da zaben raba gardama da ya gudana na neman ballewar yankin daga Iraqi, wanda ya haifar da tankiya tsakanin yankin nasu da gwamnatin Bagadaza.

Shugaban yankin Kurdawa na Iraqi Masoud Barzani yayin gangamin neman goyon bayan kada kuri'ar raba gardama ta ballewa daga kasar Iraqi.
Shugaban yankin Kurdawa na Iraqi Masoud Barzani yayin gangamin neman goyon bayan kada kuri'ar raba gardama ta ballewa daga kasar Iraqi. REUTERS/Ari Jalal
Talla

Zaben na Yankin Kurdawa mai cin gashin kan da ke arewacin Iraqi ba zai samar da yancin ballewar yankin ba kai tsaye, sai dai Kurdawan na kallonsa a matsayin wani babban ci gaba na cimma biyan bukatun su.

Dubban mutane ne suka yi tururuwa wajen kada kuri’ar a Yankin dake dauke da arzikin mai wanda yace ya gaji da hadin kan da yake da Bagadaza ganin hadin kan bai amfane su ba, a cewar shugabannin yankin.

Hukumar zaben yankin ta ce kashi 72 na masu kada kuri’u suka shiga zaben, wanda ke nuna mutane miliyan 3 da 300,000 daga cikin sama da miliyan 4 da rabi da suka yi rajista.

Shirwan Zirar, mai Magana da yawun hukumar zaben yace ana saran samun sakamako sa’oi 24 bayan kamala zaben.

Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da kungiyar kasashen Turai da kasashen Turkiya da Amurka suka bayyana damuwar su kan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.