Isa ga babban shafi
Turkiya

Shugaba Erdogan na Turkiyya na ziyara a Iran kan batun ballewar Kurdawan Iraqi

Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan na wata ziyara yau Laraba a Iran a wani mataki na tattaunawa da takwaransa Hassan Rouhani da kuma shugaban addini Ayatollahi Komeini don kawo karshen yunkurin ballewar kurdawan Iraqi da suka kada kuri’ar raba gardama a baya-bayan nan. Turkiyya da makwabciyar ta Iran na nuna adawa da matakin ballewar Kurdawan Iraqi bisa tsoron ka da hakan ya tunzura Kurdawan kasashensu su bukaci ballewa.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Iran Hassan Rouhani yayin tattaunawarsu kan yadda za su bullowa batun ballewar yankin kurdawan Iraqi.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Iran Hassan Rouhani yayin tattaunawarsu kan yadda za su bullowa batun ballewar yankin kurdawan Iraqi. Reuters
Talla

Kafin ziyarar ta Erdogan, a jiya Talata ministan harkokin wajen kasar ya sanar da cewa Turkiyya na bukatar Iraqi ta karbe iko da yankin kurdawa da ke da iyaka da Turkiyyan a arewacin Iraqi.

Haka Zalika a Lahadin da ta gabata, Shugaba Recep Tayyib Erdogan ya shaidawa majalisun kasar sa cewa zai kulla yarjejeniya da Iran kan yadda za su bullowa batun zaben raba gardamar yankin kurdawan daya gudana a Iraqi don kaucewa ballewar na su Kurdawan.

Tun a watan Augusta ne aka shirya ziyarar da Shugaba Erdogan zuwa Iran wadda za ta mai da hankali kan batun tsaro da kuma matakan da za a kara dauka don yakar kungiyar ISIS dama yadda za a kara samar da tuddan muntsira a Syria, amma a yanzu bayan shigowar batun kurdawa ya sa aka sauya akalar tattaunawar zuwa batun yadda za a shawo kan ballewar yankin na Kurdawa daga Iraqi da Iran dama Turkiyya.

Majalisar dinkin duniya da Amurka na kallon ballewar yankin na kurdawa a matsayin lamarin da ka iya kara ruruwar ayyukan kungiyoyin IS da ISIL dama yakin basasar Syria a hannu guda.

Suma dai kasashen na Iran da Turkiyya dama gwamnatin Iraqi na adawa da matakin tare da yunkurin kakabawa yankin takunkumi matukar ya ci gaba da bukatar kafa kasa mai zaman kanta.

Cikin makon daya gabata ne dai Turkiyya ta fara wani atisayen Sojin hadaka da Iraqi haka zalika ta sanar da fara wani na daban da Iran, duk da cewa dai har yanzu ba a sanar da matakin kulla yarjejeniyar atisayen Tsakanin Turkiyya da Iran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.