Ba zamu fasa kera manyan makamai masu linzami ba - Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya ce kasar zata cigaba da kera manyan makamai masu linzami, domin kare kanta daga duk wata barazana, ba kuma zata dauki matakin a matsayin sabawa wata yarjejeniyar kasa da kasa ba.
Wallafawa ranar:
Rouhani ya bayyana haka ne a yau Lahadi, yayin jawabi a kafar talabijin ta kasar.
Matsayar ta Iran ta zo ne kwanaki kadan bayanda majalisar wakilan Amurka ta amince da sake kakabawa kasar ta Iran sabbin takunkumai kan shirinta na kera manyan makamai masu linzami, don dakile yiwuwar daga likkafar kere-keren zuwa mallakar makamin nukiliya, zargin da Iran ke cigaba da musantawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu